Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira da Gajiyayyun ta Kasa (NCFRMI) ta ce ta fara shirye-shiryen kwaso ’yan asalin jihar Borno kimanin 4,982 dake gudun hijira a kasar Kamaru.
Hukumar, cikin wata sanarwa da Mai Ba ta Shawara Kan Watsa Labarai, Sadiq Abdulkateef ya fitar ranar Lahadi, ta ce daga cikin adadin, 3,224 za su koma garin Banki, sai kuma 1,758 da za su koma Bama.
Ya ce hakan ya biyo bayan umarnin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar ne na dawo da duk ’yan Najeriya dake gudun hijira a kasar ta Kamaru.
Sadiq ya ce Kwamishinan hukumar, Sanata Bashir Garba Lado a karshen makon nan ya tattauna da hukumomin kasar ta Kamaru da kuma na Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHRC) a garin Marwa na kasar ta Kamaru kan lamarin.
“Tattaunawar dai ci gaba ce a kan wadanda aka yi a shekarar 2017 da Kwamishiniyar hukumar ta wancan lokacin, kuma Ministar Jinkai a halin yanzu, Sadiya Umar-Farouk ta jagoranta, wacce kuma ta kai ga kwaso ’yan Najeriya 134 daga Kamarun.”
Sanata Lado, wanda kuma shine Shugaban Kwamitin Kwaso ’yan gudun hijirar ya ce tattaunar wata sharar fage ce ga wacce bangarori ukun za su yi a cikin wannan makon.