Majalisar Wakilai ta yi barazanar karkasa kwangilar aikin hanyar Abuja zuwa Kano da Gadar Neja ta biyu ga wasu kamfanoni saboda tafiyar hawaniyar da kamfanin Julius Berger ke yi a aikin.
Majalisar ta yi bayyana haka ne a zaman da Kwamitinta mai Kula da Ayyuka ya yi da kamfanin Julius Berger a ranar Alhamis.
Shugaban kwamitin, Abubakar Kabir Abubakar (APC, Kano) ya koka kan tsaikon da ake samu wajen aiwatar da aiyukan.
Abubakar ya ce, gwamnati ta bai wa kamfanin fiye da Naira biliyan N200 amma aikin kamar ba a yi.
Ya ce, gwamnati ta bayar da kwangilar aikin Gadar Neja ta Biyu a kan Naira biliyan N206.151, sai hanyar Kaduna zuwa Abuja a kan Naira biliyan N155, da kuma bangaren farko na hanyar Lagos zuwa Ibadan a kan kudi Naira biliyan N134.
Dan Majalisar ya ce yanayin yadda kamfanin ke tafiyar da aikin ya nuna ba zai iya gama shi da wuri ba har Shugaba Buhari ya kaddamar da shi kafin karewar wa’din mulkinsa.
“Mun bayar da shawarar a karkasa wadannan ayyukan ga kamfanoni daban-daban saboda ba na tsammanin Julius Berger kadai za ta iya kammala shi”, inji shi.
Da yake kare kamfanisa, Shugaban Gudanarwa na Julius Berger Nigeria Plc, Las Riechter, ya yi alkawarin kammala ayyukan cikin kayyadadden lokutansu.
Ya ce kowace kwangila da aka ba su tana da nata kayadadden lokacin kammalawa.