Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce daga watan Disamba mai kamawa za a haramta ayyukan baburan Keke-NAPEP a garin Abuja.
Wike ya ce shirye-shirye sun yi nisa domin fito da sabbin motocin daukar mutane a kwaryar birnin Abuja daga wata mai zuwan.
Ya ce da zarar motocin gwamnatin sun fara aiki za a bukaci masu Keke-NAPEP su koma kauyukan Abuja da aiki.
“Na san yanzu matuka Keke-NAPEP za su fara cewa an toshe musu hanyar neman kudi, to amma dole mu dakatar da su domin inganta birnin Abuja, da samar da cikakken tsaro a birnin,” in ji ministan.
- Najeriya za ta fara fitar da tataccen mai kasar waje a 2024 —NNPCL
- Hukuncin da muka zartar na korar Gwamnan Kano na nan daram – Kotu
Wike ya bayyana hakan ne ranar talata, lokacin da yake ganawa ta musamman da masu tsara taswira da gina gidaje a Abuja, inda ya ce hakan zai rage matsalar tsaro a birnin.
“Ina tabbatar muku idan motocin mu suka fara aiki matsalar kwace a cikin motocin haya za ta kau.
“Motocinmu za su rika zirga-zirga ne a hanyoyin Maitama, Asokoro da sauran sassan kwaryar birnin Abuja” inji Ministan Abuja.