Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ce nan ba da jumawa ba za a koma sayar da tikicin jirgin kasa ta intanet.
Ameachi ya sanar da hakan ne yayin bayanin sabbin dokokin hawa jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da za a bude ranar daga Laraba 29 ga watan Yuli 2020.
“Nan da wata biyu zuwa uku za mu fara sayar da tikiti ta intanet ba sai an zo tasha ba, don haka babu batun yadda za a bayar da tazara a layin sayen tikiti”, inji shi.
Ya bayyana sabbin dokokin ne a lokacin jawabinsa ga taron kwamitin kar-ta-kwana ka cutar COVID-19 a ranar Litinin kamar haka:
Sanya takunkumi:
Jazaman ne kowa ya sanya takunkumi ya rufe bakinsa da hancinsa.
“Takunkumin baki kawai ’yan Najeriya suke sakawa, idan ka sa irinsa jirgi zai tsaya jami’an tsaro su sauke ka”, inji shi.
Abun tsaftace hannu:
Ba za a bari kowa ya shiga tashar jirgi ba sai yana dauke da abun tsaftace hannu yana kuma sanye da takunkumi.
“Dole abun wanke hanunka ya kasance alkohol din da ke cikinsa bai gaza kashi 79 ba.
“Duk sai mun duba, kuma ni da kaina zan kasance a wurin a ranar Laraba”, inji ministan.
Fasinjoji 50 kacal:
An rage adadin fasinjojin da kowane tarago zai dauka zuwa 50 daga 88 da ake dauka a baya.
Rage adadin fasinjojin zai tabbatar da bayar da tazara bisa tsarin COVID-19.
Sabon kudin tikiti:
Ministan ya ce an kafara farashin tikicin jirgi saboda an rage yawan mutanen da ake dauka.
“Shi ya sa muka kara farashin tikitin karamar kujera daga N1,500 zuwa N3,000, matsakaiciya kuma N5,000 sa’annan babbar kujera N6,000”.
Jiran jirgi a tasha:
Duk wanda bai samu kujera a dakin da ake zama a jira jirgi ba sai dai ya fita waje ya jira.
“Mutum uku kacal za su zauna a kowane benci ba uku ba”, a cewarsa.
Babu yawo a cikin jirgi:
Zuwa bayi kadai aka yarda mutum ya tashi ya je domin ba a yarda da kai-komo a cikin jirgi ba.
Jami’an tsaro:
Ministan ya ce an kara yawan jami’an tsaro a cikin jiragen domin tabbatar da bin dokokin da hukunta masu karyawa.
Sabon salo:
Daga karshe ya ce nan ba da jimawa ba za a koma sayar da tikitin jirgin kasa ta intanet.
Amaechi ya ce bai so bude tashoshin jirgin a ba, “amma na sake tunani saboda matsin da na yi ta samu daga masu son yin tafiye-tafiye domin bukukuwan Babbar Sallah, shi ya sa na yarda a bude titin jirgin Abuja zuwa Kaduna”.