Gwamnatin Najeriya za ta kashe naira biliyan 863 wurin gudanar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma na karshen shekara.
Shirye-shirye ne na musamman da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo dasu da nufin rage wa ’yan kasar radadin talauci.
- Birtaniya ta gargadi ’yan kasarta kan zuwa wasu jihohi 12 a Najeriya
- Buhari ya jajanta wa Amurka kan mutuwar Colin Powell
Shirin National Social Investments Programmes (NSIP) da ya kunshi shirin N-Power da Conditional Cash Transfer Programme (CCT), da kuma shirin raba basussuka ga kananan ’yan kasuwa zai lakume naira biliyan 410.
Za a kuma kashe karin naira biliyan 300 kan wasu shirye-shiryen na daban ga al’umma a karkashin kulawar Ma’aikatar Ayyukan Jin Kai da Kare Afkuwar Bala’i.
Tun a shekarar 2016 ne gwamnati mai ci a Najeriya ta bullo da shirye-shiryen tallafa wa ’yan kasarta don rage musu radadin matsin rayuwa da suke ciki.
Kuma a 2020 abubuwa sun dada nauyi ga ’yan Najeriya bayan bullar annobar Coronavirus, da ta yi illa ga tattalin arziki.