✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kashe biliyan 7.3 wajen sabbin hanyoyi a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ware kimanin Naira biliyan 7.3 domin gina sabbin hanyoyin a cikin jihar. Wannan kasafin na kunshe ne a cikin kasafin kudin…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ware kimanin Naira biliyan 7.3 domin gina sabbin hanyoyin a cikin jihar.

Wannan kasafin na kunshe ne a cikin kasafin kudin bana wanda gwamna El-Rufai ya gabatar, sannan majalisar jihar ta amince da shi kamar yadda kamfanin dillancin labarai ya ruwaito.

Hakanan kuma kasafin ya nuna cewa an ware kimanin Naira biliyan 2.1 domin samar da hasken wuta a titin, sai kuma Naira miliyan 23 domin kula da wutar.