✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kara wa ’yan sanda albashi

Buhari ya ba da umarnin fito da sabon albashi da alawus din ’yan sanda

Shugaba Buhari ya umarci Hukumar Tsara Albashi ta Kasa da ta fito da sabon tsarin albashi da alawus-alawus na jami’an ’yan sanda a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a bukin yaye kananan hafsoshin ’yan sanda 418 karo na uku da ya gudana a Kwalejin ’Yan Sanda da ke Wudil a Jihar Kano, ta bakin Ministan Ayyukan ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi.

Shugaban ya jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da daukar jami’an ’yan sanda 10,000 a kowace shekara da nufin magance matsalar karancin jami’an tsaron da rundunar ke fama da ita.

Ya kuma bayyana cewa a yanzu an sake farfado da Kwamitin Karbar Koke-koken Jama’a batun cin zarafi da take hakki daga jami’an ’yan sanda.