✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kara mafi karancin albashi daga N30,000 —Ngige

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kara wa ma'aikata albashi bisa la'akari da tsadar rayuwa da ake fama da ita a fadin duniya

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kara mafi karancin albashin ma’aikatanta daga Naira 30,000.

Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya ce gwamnati za ta kara albashin ne bisa la’akari da karin tsadar rayuwa da ake ciki a yanzu, domin kara wa ma’aikatan karfin aljihu.

Ngige ya ce, “An samu hauhawar farashin abubuwa a fadin duniya, saboda haka za mu kara albashi daidai da abin da ke faruwa; Da ma Dokar Kwadago to 2019 na da sabon sashe da ya yi maganar gyaran fuska.

“An fara yin karin ne ga malaman jami’o’i saboda halin da suke ciki tsakaninsu da gwamnati da ma’aikatar ilimi, batu ne tattaunawa.

Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) dai ta haura wata shida tana yajin aiki saboda abin da ta kira saba alkawura da gwamnati ta yi mata na biyan bukatunsu.

Bukatun malaman sun hada da neman hakkokinsu da suke bin ta bashi, karin albashi, kuma kudaden inganta harkokin karatu a makarantun da sauransu.

Amma da yake jawabi, Ngige ya ce, “A bisa tsarin yin tayi da yarda, ASUU za iya mika mana abin da suke so mu kuma sai mu duba.

“A halin yanzu dai ba su ce mana komana amma idan suka kawo kuma dole mu duba domin a samu mafita a daidaita.’’

Ya bayyana haka ne a jawabinsa ga Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) a taron kaddamar da littafi kan tarihin gwagwarmayar ’yan kwadago mai suna Contemporary History of Working Class Struggles, da ya gudana a Abuja.

A shekarar 2019 ne dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Da yake jawabi a taron, tsohon Shugaban NLC na Kasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya shawarci ’yankungiyar da su tsaura bincike kan manufofi da tsare-tsaren tattalin arzikin ’yan takarar zaben 2023 da ke kara matsowa.

A cewarsa, “Babu abin takaici gare ku a matsayinku na ma’aikata, fiye da a zabi mutum daga cikinku, amma ya zama abubuwan da yake yi sun ci karo da manufofinku.”