Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam dake Kano, Barista Abba Hikima ya sha alwashin kai ƙarar masu tunzura matashin nan Ale Rufai mai Gangayaliyon.
A baya bayan ne dai bidiyon Ale Rufai suka karaɗe soshiyal midiya inda yake ambaton adadin kuɗi da suka zarta hankali irinsu Gangaliyon da Auwaliyon.
Matashin ɗan Birnin Kano da yake ciniki a Kasuwar Kurmi ya samu lalurar ƙwaƙwalwa ne tun ya na makarantar sakandire.
Hisbah ta cafke masu shirin daura auren jinsi a Kano
Bidiyon Dala ba zai hana Ganduje muƙami ba – Muhammad Garba
Ale Rufai ya na riya cewa babu mai kuɗinsa a duk duniya, duk da halin da yake ciki akwai alamun matsin rayuwa.
Wannan ya sa ƴan soshiyal midiya suke ta yi masa bidiyo ya na sayen manyan kamfanoni da muhimman wurare.
Kawo yanzu dai idan aka daka ta waɗanann bidiyoyin, Ale Rufai ya saye jihohin Kano, Kaduna da Jigawa.
Haka kuma a bidiyoyin Ale Rufai na ambata cewa ya saye kamfanonin Ɗangote da BUA.
Neman Magani
Bayan da bidiyoyin suka yaɗu sai kuma wasu masu jin ƙai suka fara neman haɗa gidauniya domin tallafawa a nema masa magani.
A nan ne ƴan uwansa suka magantu a shafukan Facebook da ma gidajen rediyo a Kano, inda suka ce su na iya bakin ƙoƙarinsu na kula da shi.
Sannan sun buƙaci mutane da su daina tunzara shi saboda hakan na ƙara tsananta lalurarsa.
Da safiyar Litinin ne kuma, Barista Abba Hikima ya gargaɗi masu tunzara shi cewa zai gurfanar da su gaban shari’a idan ba su daina ba.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abba Hikimi ya ce likitoci sun tabbatar cewa tsokanar da ake masa na ƙara masa rashin lafiyar dake damunsa.
Ya ce “Wannan rashin tsari ne da sanin ya kamata. Inda ɗan uwan masu yin hakan ne babu wanda zai bari a dinga wulaƙanta shi haka. Sai ka ce ba Musulmi ba?