Majalisar Wakilai ta fara shirin kafa dokar hukuncin daurin shekara biyar ga duk wanda aka kama da laifin yi wa mata kaciya a Najeriya.
Tuni dai kudirin dokar ayyana yyin kaciyar mata a matsayin babban laifi a Najeriya ya tsallake matakin karatu na biyu a Majalisar a ranar Laraba.
- Yadda uba da dansa suka lakada wa likita duka a asibiti
- An yi masa daurin rai da rai kan yi wa ’yar makwabcinsa mai shekara 14 fyade
Manufar dokar kamar yadda Honarabul Ganiyu Johnson ya gabatar wa Majalisar, ita ce yi wa Dokar Haramta Cin Zarafin Mutane (VAP) ta 2015 gyara ta yadda za a tsananta hukuncin ga masu yi wa mata kaciya.
Ya ce dokar na bukatar a sanya hukuncin daurin shekara biyar a kurkuku ko kuma tarar Naira miliyan daya ga duk wanda aka samu da hannu a ciki.
Ganiyu ya ce so yake wannan doka ta yi aiki a kan duk wanda aka samu ya yi wa mace kaciya ko ya sa aka yi.
Don haka ya ce, yi wa Sashe na 6(2) na dokar kwaskwarima zai taimaka wajen dakile harkar kaciyar mata a da cin zarafin kananan yara.