Wani malamin coci da ke Jihar Akwa Ibom, ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zarginsa da yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyade, bayan mijin yayarta ya kai ta cocinsa domin ya yi mata addu’a.
Wanda ake zargin Nse Thompson, mai shekaru 32 na da ’ya’ya uku, kuma ya fito ne daga Ikot offiong Nsit da ke Karamar Hukumar Nsit Ibom.
- NAFDAC ta kama dan kasuwa da maganin Maleriya na jabu a Onitsha
- Badakalar N2.9bn: Kotu ta ba da belin Okorocha kan N500m
Rahotanni sun ce ya tafi da yarinyar gidansa da sunan yi mata addu’a, karshe ya bige da yi mata fyade tsawon daren.
Da take ba wa kotun bayanin yadda lamarin ya faru, yarinyar da ke aji daya a babbar makarantar sakandare da ke Uyo, ta ce mijin yayarta ne ya kai ta cocin malamin ranar Juma’a domin ya yi mata addu’a, da niyyar ya zo daukar ta bayan awa guda.
To sai dai a cewarta barinsa harabar majami’ar ke da wuya malamin cocin ya kira mai babur mai kafa uku, ya ce ta shiga domin akwai wasu mutane biyu da zai yi wa addu’ar kan ya zo kanta.
Ta ci gaba da cewa “Mun je ya yi musu addu’ar, daga nan ne muka fita daga gurin a kafa har zuwa bakin titi, inda yake tare da wani mai Napep din, da muka je wani guri sai ya tsaida mai babur din, ya ce na jira shi.
“Ya sauka ya shiga wani gida, sannan ya leko ya ce na shigo, ya kai ni wani daki, ya kulle kofa ya ce sai na tube”, inji yarinyar.
Bayan sauraron jawabin yarinyar ne mai shari’a Bassey Nkanang ya dage zaman kotun zuwa ranar daya ga watan Agustan 2022, domin ci gaba da bincike.