✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a jefe tsoho mai shekara 60 saboda fyade a Kano

Kotun Musulunci ta yanke masa hukuncin rajamu bayan ya amsa cewa ya aikata fyade

Wata kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa wani tsoho mai shekara 60 hukuncin kisa ta hanyar jefewa bayan samunsa da laifin yin fyade.

Kotun, mai zamanta a Kofar Kudu ta yanke wa tsohon Mati Audu hukuncin ne a zamanta na ranar Laraba.

Alkalin kotun, Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin ne bayan da tsohon dan asalin yankin Falsa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa a Jihar ya amsa laifin da kansa.

Tun da farko dai an zargi tsohon ne da yi wa wata yarinya mai kimanin shekaru 12 fyade, laifin da ya yi ikirarin aikatawa a zama daban-daban har karo uku.

Alkalin ya ce hukuncin ya yi daidai da tsarin Shari’ar Musulunci da ya tanadi hukuncin rajamu kan duk wanda aka samu da aikata zina matukar dai ya taba yin aure.

Hukuncin na zuwa ne kwana biyu bayan wata kotun Shari’ar Muslunci ta yanke wa wani matashi mai suna Yahaya Sharif Aminu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin batanci ga Ma’aiki (SAW).