Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce za a iya magance rikicin ku giyar Boko Haram ta hanyar siyasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan ya tattauna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
- Sarkin Zazzau: Kotu ta tabbatar da nadin Bamalli
- Kotu ta raba auren shekaru 12 saboda miji ya ki neman aiki yi
A yayin ganawar Gwamnan da shugaba Buhari kan kalubalen tsaron da jihar ke fuskanta, ya ce “Tunkarar matsalar da karfin tuwo ba zai magance matsalar ba duka.”
Zulum ya bukaci dukkan matakan gwamnatoci da su samar wa da matasa ayyukan yi don kaucewa masu samun damar shiga gonakin jama’a su aikata sace-sacen amfanin gona.
Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa jama’ar jihar da suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira sun koma garuruwansu domin su ci gaba da yin noma a gonankinsu da kuma rayuwa kamar yadda suka saba.