Jami’an ‘Yan Sanda a kasar Italiya sun fara gudanar da bincike kan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Ronaldo bisa karya dokar Coronavirus.
Wata na’urar bin diddigin tafiyar mutum a ababen hawa ce dai ta gano cewar Ronaldo da budurwarsa Georgina Rodriguez sun yi balaguro daga Piedmont zuwa yankin Valle d’Aosta, dake kasar Italiya.
- Ronaldo ya zama dan kwallo na biyu mafi zira kwallaye a tarihi
- Kocin Real Madrid Zidane ya kamu da Coronavirus
- Barcelona za ta dauko Aguero, Chelsea na son Dembele, Ahmed Musa zai fara karbar horo a West Brom
- Real Madrid na dab da dauko Alaba daga Bayern Munich
Ronaldo da budurwar tasa dai sun tafi yankin ne don yin bikin zagayowar ranar haihuwarta.
Tuni dai hotonsu ya karade kafafen sada zumunta na zamani wanda hakan ya janyo da cece-kuce mai yawa.
Tun bayan sake bullar cutar COVID-19 a karo na biyu, kungiyoyin kwallon da da dama a kasar Italiya suka sanya wa ‘yan wasansu dokar takaita tafiye-tafiye.
Hakan na daga cikin irin matakan da gwamnatin kasar ta baya saboda rage cunkoson mutane, musamman ga ‘yan kwallon kafa.
Kazalika, yankin da Ronaldo suka je tare da budurwarsa na daga cikin yankin da aka sanya wa dokar kulle.
Idan har jami’an tsaro suka tabbatar da laifin nasa, za a iya cin sa tara ko kuma daurin watanni uku a gidan yari.