Gwamnatin Kasar Spain ta sha alwashin haramta sana’ar karuwanci a kasar kan abin da ta bayyana a matsayin hakan wata hanya ce ta bautar da ’ya’ya mata.
Firaiministan kasar, Pedro Sanchez ne ya bayyana yayin da yake tsokaci a wajen rufe taron jam’iyyarsa na kwanaki uku da aka gudanar a birnin Valencia.
Sanchez ya yi wa mahalarta taron alkawarin cewa zai aiwatar da shirin haramta karuwanci a fadin kasar kan abin da ya kira yaddda mummunar dabi’ar ke zama wata hanya da bautar da mata.
A cewarsa, manufofin da gwamnatinsa ta gabatar sun taka rawar gani wajen shawo kan rikice-rikicen da ake samu da kuma batun karin albashi.
Sashen Hausa na Rediyon Faransa ya ruwaito cewa, har kawo yanzu babu wata doka da ta hana biyan kudi a bainar jama’a domin daukar matar da za a yi lalata da ita, sai dai dokar da ta hana safarar mata.
Kazalika, dokokin Spain basu amince da karuwanci a matsayin sana’a ba, amma kuma akwai gidajen karuwai da dama a fadin kasar, inda wasu ake samunsu a matsayin Otel, wasu kuma gidan kwana ne kawai.
Wasu alkaluma da Hukumar Binciken Kasar ta fitar sun bayyana cewa, akalla kowane mutum daya cikin mazaje uku da ke kasar, ya taba biyan kudi akalla sau guda a rayuwarsa domin yin lalata da mace kamar yadda binciken da aka gudanar a shekarar 2009 ya nuna.