✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za A Haramta Hawa Babur Mai Taya Biyu A Yobe

Gwamnati da hadin gwiwar jami'an tsaro sun haramta hawa babur mai kafa biyu a wasu kakanan hukumomi hudu na Jihar Yobe.

Bisa ga dukkannin alamu murna za komawa ciki a wasu hananan hukumomin hudu na Jihar Yobe  inda gwamnatin jihar ke shirin dakatar da amfani da babura masu tayoyi biyu.

Gwamnatin jihar da hadin gwiwar jami’an tsaro sun dauki matakin ne a kananan hukumomin Fika, Fune da Gujba da kuma Gulani da nufin rage aikata laifuka.

Haka na zuwa ne bayan hare-haren ranar Litinin da suka yi sanadin kashe mutum daya, tare da kona gidaje kimanin 146, mutane 1,686 suka rasa muhallinsu a Karamar Hukumar Fika.

Mataimakin gwamna, Hon Idi Barde Gubana ya ce haramta amfani da baburan na daga cikin kudirori  14 da suka aka amince da shi a taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro na jihar.

Idi Barde Gubana ya shaida wa manema labarai cewa Zaman nasu ya samu halarcin sarakunan jihar da shugabannin hukumomin tsaro da kuma kwamishinan ’yan sandan jihar, Ahmed Garba.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar da abokan huldar jami’an tsaron jihar  sun amince da dakatar da amfani da babura a kananan hukumomi hudu da ke kan gaba wajen matsalolin tsaro a jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce rikicin baya-bayan nan da aka samu a kananan hukumomin Fika da Fune, musamman a kauyen Gurjaje, ba rikicin kabilanci ba ne, sai dai ya haifar da shigowar bakin haure.

Ya ce maharan sun yi amfani da babura wajen kai wa manoma hari da daddare, inda ya ce za a sake duba yadda ake tafiyar da bakin haure da ke zuwa daga jihohin makwabta don gudun sake tabarbarewar tsaro a jihar.