Kwamitin da Hukumar FIFA ta kafa wanda zai kula da yadda gasar cin kofin duniya a katar a shekarar 2022 ya bayar da shawarar a gudanar da gasar a watan Nuwamban shekarar 2022 saboda yanayin tsananin zafi da kasar ke fuskanta a watannin Yuni da Yuli.
Da ma ana gudanar da gasar ce a watan Yuni zuwa na Yuli a duk shekarar da za a yi, amma ganin yadda katar take da tsananin zafi ta sa FIFA ta yi nazarin takamaiman lokacin da ya dace a gudanar da gasar a katar.
Sai dai kafin a cimma wannan matsaya ta gudanar da gasar a watan Nuwamba, wasu kwamitoci sun ba hukumar FIFA shawarar a wadata daukacin filayen wasannin da na’urar sanyaya daki watau air condition da kuma a dakunan kwanan baki a otel-otel da gidajen saukar baki da sauran wurare amma daga baya aka yi nazarin wannan ba zai canza komai ba, musamman ga bakin da za su kwarara zuwa kasar don kallon yadda gasar za ta kaya. Hasalima an ce ba kowane bako ne yake da damar da zai sauka a otel ko gidajen saukar da baki na musamman da gwamnati za ta samar ba. Idan kuwa haka ne, ya nuna sauran talakawa za su shiga halin ni ’yasu kenan a yayin gasar.
Akan haka ne Hukumar FIFA ta kafa kwamitin da zai ba ta shawara a kan takamaiman lokacin da ya dace a gudanar da gasar, musamman lokacin hunturu da hakan ya sa kwamitin ya amince da a fara gasar a ranar 26 ga watan Nuwamba zuwa 23 ga Disamban 2022.
Sai dai kungiyoyin kwallon kafa na Nahiyar Turai sun koka a kan lokacin don suna ganin hakan ba karamin cikas zai kawo musu a jadawalin gasar rukuni-rukuni da kuma na gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai ba idan aka gudanar da gasar a Nuwamban shekarar 2022.
Tuni shugaban Hukumar kwallo ta Nahiyar Asiya da ya shugabanci kwamitin kula da yadda gasar cin kofin duniya da za a yi a katar a 2022 Sheikh Salman bin Ebrahim Al-Khalifa ya tabbatar cewa kwamitinsu ya amince da a gudanar da gasar a watan Nuwamban 2022.
Ana sa ran Hukumar FIFA za ta amince da ranakun da kwamitin ya gabatar mana ne a watan gobe a taron da za ta yi a hedkwatar hukumar da ke Zurich a Suwizilan.