✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a gina wa malaman makaranta gidaje 5,000 a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta gina wa malaman makarantun firamare da na sakandare gidaje 5,000 a jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta gina wa malaman makarantun firamare da na sakandare gidaje 5,000 a jihar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a kan harkar ilimi da ya gudana a Fadar Gwamnatin jihar ranar Asabar.

A cewar Gwamnan, rukunin farko na  aiki wanda aka yi wa lakabi da TRA za a yi shi ne da nufin samar da muhallai ga malaman da kuma iyalansu.

Ya ce shirin zai gudana ne a matsayin hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar, Kamfanin Family Homes Funds da kuma bankin Federal Mortgage Bank.

“Dukkan kananan hukumomi 36 da wajen birni za a gina musu gidaje 100 kowacce, yayin da na cikin birnin kuma za a gina wa kowacce gidaje 150,” inji gwamnan.

Ganduje ya kuma ce gwamnatinsa za ta samar da filaye, ruwan sha, wutar lantarki da hanyoyi yayin da sauran abubuwan kuma kamfanonin ne za su samar.

A cewarsa, aikin wanda za a fara shi a shekarar 2021 zai kasance na zabi ga masu sha’awar cin gajiyarsa, kuma za su rika biya da kadan-kadan.

Tuni dai aka kafa kwamitin da zai kula da gudanar da aikin karkashin jagorancin Rabi’u Sulaiman Bichi.

Da yake jawabi a wurin taron, Rabi’u Bichi ya ce an bullo da shirin ne domin ya dace da manufar gwamnatin jihar ta samar da ilimi kyauta kuma dole.

“Rabon da a gina makamantan wadannan gidajen a Kano tun zamanin turawan mulkin mallaka.”

Bichi ya kuma ce jihar za ta nemi tallafin Gwamnatin Tarayya domin ganin nasarar shirin.