✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gina matatar mai a Akwa Ibom

Kamfanin Blooming Faith Petroleum Limited da ke yankin Hong Kong na kasar China ya ce, tare da hadin guiwar Gwamnatin Tarayya ya kammala shirye-shiryen gina…

Kamfanin Blooming Faith Petroleum Limited da ke yankin Hong Kong na kasar China ya ce, tare da hadin guiwar Gwamnatin Tarayya ya kammala shirye-shiryen gina matatar mai a Jihar Akwa Ibom.
Sabuwar matatar wanda za ta rika tace danyen man fetur kimanin ganga dubu 200 a kullum, za a gina ta ne don biyan bukatun ’yan kasar ta fuskar wadatuwa da man fetur.
Shugaban Kamfanin Dokta Robert Yeung  ya shaida wa manema labarai cewa suna da kwarin guiwa kwalliya za ta biya kudin sabulu saboda kasar nan babban kasuwa ce a nahiyar Afirka.
Ya ce sun gabatar da bukatarsu ga kamfanin man kasar nan wato NNPC don neman goyon bayansa.
A karshe ya ce “idan aka amince da gina matatar, za ta zama ita ce ta biyu wajen yawan tace danyen mai a kasar nan, wato bayan wadda Alhaji Aliko dangote yake kan aikin ginawa, wadda ake fatan za ta fara aiki a shekarar 2019”.