✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a gina birikin sojin ruwa a Kano

Gwamnatin Kano ta ba da filin da za a gina barikin sojin ruwan.

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya za ta gina barikin sojinta a Jihar Kano a wani yunkuri na kara samar da tsaro a Jihar.

Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo, ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Laraba.

Babban Hafsan, wanda ke halartar taron kwana hudu da rundunar ta shirya a Kano, ya ce, “Kwamitin gudanarwar Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ya amince a gina barikin sojin ruwa a Kano, da ma wasu wuraren.

“Mun nada Kyaftin Muhammad Abubakar Alhassan a matsayin Mukaddashin Kwamandan Rundunar, kuma daga yanzu zai kasance a cikin tsare-tsaren tsaron jihar,” inji shi.

Babban Hafsan ya yi wa Gwamna Ganduje godiya kan fili mai girman kadada 100 da ya bayar domin a gina sansanin sojin ruwan.

A nashi jawabin, Gwamna Ganduje ya yaba wa rundunar da ta ga dacewar Kano a matsayin wurin gudanar da taron.

“Hakan ya nuna irin kwarin gwiwar da kuke da shi game da samar da tsaro a Jihar, wanda kuma sako ne cewa Kano na cikin tsaro da aminci.

“Mun gode da kuka zabi Kano domin gina sansanin sojin ruwa wanda abu ne mai matukar muhimmanci.

“Wannan ya kara mana kwarin gwiwa cewa za a samu tsaro yadda ake bukata a jiharmu,” inji Ganduje.

Babban Hafsan Sojin Ruwan ya ziyarci Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, kafin halartar laccar da rundunar ta shirya gudanarwa kan tsaron teku da dangoginsu.

Tun a ranar Talata, rundunar ta gudanar da wasu taruka a Jihar inda ta kwadaitar da matasa kan muhimmancin su shiga aikin sojin ruwa.

Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ta yi kamari, ciki har da jihohin Katsina da Kaduna masu makwabtaka da Kano.

Sabanin makwabtanta, a Jihar Kano ba a fiye samun matsalar garkuwa da mutane ba, duk da cewa tana fama da matsalar masu kwacen waya da ’yan daba da sauransu.