✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fuskanci karin ambaliyar ruwa cikin wata 2 masu zuwa a Najeriya — NiMet

Hukumar ta ce 'yan Najeriya ba sa amfani da hasashen yanayi

Shugaban Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) Farfesa Mansur Bako Matazu, ya gargadi ’yan Najeriya da su shirya fuskantar karin ambaliyar ruwa a watanni biyu masu zuwa.

Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talbijin din Channels ranar Litinin, lokacin da yake bayani kan irin barnar da ambaliyar ta yi a Najeriya a ’yan makonnin nan.

Shugaban ya ce tun a baya hukumar ta sha fitar da gargadi iri-iri ga ’yan Najeriya kan barazanar amma suka yi shakulatin-bangaro da ita.

Farfesa Matazu ya ce mutane na ci gaba da sare bishiyoyi da zubar da shara a magudanun ruwa.

Ya ce, “Za a sami karin saukar ruwan sama a watanni biyu masu zuwa. Wannan shi ne lokacin da za a fi samun ruwan – Yuli, Agusta da Satumba. Za mu fuskanci karin ambaliyar ruwa.

“Muna ganin abubuwan da ke kawo kalubale ga sauyin yanayi, don haka ya zama wajibi mutane su rika kwashe shara.

“Muna ba hukumomi da ma’aikatun gwamnati shawara kan su gargadi mutanen da ke wuraren da ke da barazanar ambaliyar da su kaurace musu,” inji shi.

Shugaban na NiMeT ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su fara daukar hasashen yanayi da muhimmanci.

%d bloggers like this: