Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu kan dokar yanke hukuncin daurin rai da rai ga masu garkuwa da mutane.
Kudurin dokar ta kuma tanadi hukuncin daurin shekara 30 ga masu hannu da wadanda aka ba su wani abu daga cikin kudin fansa, baya ga daurin ra ida rai ga duk wanda ya yi garkuwa da wani har ta kai ga mutuwar wanda aka sacen.
Mai gabatar da kudurin dokar, Santa Ibikunle Amosun, ya ce dokar za ta samar da tsattsauran hukunci domin yin maganin masu garkuwa ko taimaka musu, musamman ganin yadda matsalar ke kara kamari a Najeriya.
Amosun ya ce rashin yanke tsauraran hukunci a kan masu garkuwa da mutane ne ya sa matsalar ke ci gaba da karuwa.
“A kokarin hana hakan ne ake bukatar yanke irin wannan hukunci mai tsanani ga masu gakuwa da mutane, inda za a iya yanke musu hukuncin daurin shekara 30,” inji shi.