✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara tseren duniya na farko a Najeriya a watan Afrilu

Kwamitin shirya Gasar Tseren Duniya a Najeriya ya sanya Asabar, 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye na farko…

Kwamitin shirya Gasar Tseren Duniya a Najeriya ya sanya Asabar, 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye na farko na tseren a Abuja.

Daraktan  tseren, Olukuyade Thomas, ya ce kwamitin ya sanya ranar ce bayan ganawa da masu daukar nauyi gasar da Hukumar Birnin Tarayya da kuma masu tseren na cikin gida da na kasashen waje.

Thomas ya ce rukuni uku za a gudanar a ranar farko, da suka hada da kilomita biyar da kilomita 10 da kuma kilomita 42.195.

Haka kuma akwai abubuwan nishadi da burgewa da dama da za a gudanar yayin tseren.

A baya dai an sanya watan Disambar 2022 ne a matsayin lokacin tseren, amma aka dage shi bayan sanarwar da Amurka ta fitar a wancan lokaci cewa ’yan ta‘adda za su kai hari a Abuja.