Kwamitin shirya Gasar Tseren Duniya a Najeriya ya sanya Asabar, 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye na farko na tseren a Abuja.
Daraktan tseren, Olukuyade Thomas, ya ce kwamitin ya sanya ranar ce bayan ganawa da masu daukar nauyi gasar da Hukumar Birnin Tarayya da kuma masu tseren na cikin gida da na kasashen waje.
- An gurfanar da ’yan bangar siyasa 10 a Sakkwato
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalolin Harkar Kudi Ta Intanet
Thomas ya ce rukuni uku za a gudanar a ranar farko, da suka hada da kilomita biyar da kilomita 10 da kuma kilomita 42.195.
Haka kuma akwai abubuwan nishadi da burgewa da dama da za a gudanar yayin tseren.
A baya dai an sanya watan Disambar 2022 ne a matsayin lokacin tseren, amma aka dage shi bayan sanarwar da Amurka ta fitar a wancan lokaci cewa ’yan ta‘adda za su kai hari a Abuja.