Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce za a fara shari’ar ’yan kungiyar Boko Haram da aka kama a ranar Litinin, wacce ta yi daidai da tara ga watan Oktoban shekarar da muke ciki.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Othman Salihu Isah, jiya, ministan ya bayyana cewa ’yan Boko Haram dubu daya da dari shida da saba’in wadanda ake tsare da su a wuri na musamman da ke garin Ka’inji a jihar Neja za su kasance na farko da za a fara shar’arsu.
Ya ce babban jojin gwamnatin tarayya ya nada alkalai hudu da za su saurari shari’ar.
Ya bayyana cewa Ministan Shari’ar ya amince da jerin sunayen masu gabatar da kara da za su gabatar da kararrakin a kotu.