✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara rigakafin cutar zazzabin cizon sauro

Za a fara rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a Karamar Hukumar Ifelodun da ke jihar Kwara a ranar 30 ga watan Satumban shekarar da muke…

Za a fara rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a Karamar Hukumar Ifelodun da ke jihar Kwara a ranar 30 ga watan Satumban shekarar da muke ciki don kawar da yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Karamar Hukumar Ifelodun wuri ne da wata yarin ta taba kamuwa da cutar a ranar 12 ga watan Satumba.
Rigakafin zai hada da kewayen karamar hukumar kamar yadda cibiyar yaki da cututtuka ta kasa ta bayyana a ranar Litinin.