✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara neman man fetur a Tafkin Chadi

nan ba da jimawa ba Gwamnatin Tarayya za ta fara neman mai a yankin tafkin Chadi.

Minista a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva ya ce nan ba da jimawa ba Gwamnatin Tarayya za ta fara neman mai a yankin tafkin Chadi.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake wa ‘yan jarida jawabi jim kadan bayan zantawarsa da Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai a shalkwatar rundunar tsaro ta Operation Lafiya Dole dake birnin Maiduguri.

Ministan ya kuma ce ci gaban aikin samar da zaman lafiya da aka samu a jihar Borno da yankin tafkin shine ya karfafa musu gwiwar duba yuwuwar fara aikin.

Daga nan sai ya nemi hadin gwiwar Babban Hafsan Sojin wurin samar da tsaro ga ma’aikata da kuma kayyakinsu da zarar an fara aikin.

Timipre ya ce, “Muna so mu fara aikin nema da kuma hako danyen man fetur a nan saboda mun yi amanna an sami isasshen zaman lafiyan da zai ba mu damar ci gaba da hakan a yankin Arewa Maso Gabas.

“Kamar yadda ku ka sani, tuni muka gano mai a jihar Gombe, kuma mun tabbata akwai shi a tafkin Chadi.

“Akwai alamun nasara matuka a wurin, hakan ne ma yasa muke kokarin yin hadin gwiwa da Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya domin samar da tsaro kafin fara aikin a kwanan nan,” inji Sylva.

Daga nan sai ya yabawa jajircewar sojojin kasa na Najeriya musamman wajen yaki da ‘yan ta da kayar baya a yankin Arewa Maso Gabas.

Yayin ziyarar dai, ministan ya sami rakiyar shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari da kuma Babban Manaja sashen gano danyen mai, Mohammed Ali da ma sauran manyan jami’an kamfanin.