✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara musayar dalibai tsakanin makarantar jikan Inyass da ta Izala a Zariya

Malamin ya ce wurin zai kara hada kan musulmi ya kuma rage yawan gaba a tsakaninsu

Daya daga cikin jikokin fitaccen Shehunnan nan a Darikar Tijjaniyya a duniya, Sheikh Ibrahim Inyass, wato Sheikh Abdullahi Bin Sheikh Al-Amin Inyass, ya ziyarci wata makaranta ta Izala da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Yayin ziyarar da malamin, wanda ya zo daga kasar Senegal ya kai makarantar mai suna Nurul Tilawa a ranar Asabar, ya kuma yi alkawarin fara shirin musayar dalibai a tsakaninsu.

Ba kasafai dai ake samun irin wannan ziyara tsakanin malaman bangarorin biyu ba, musamman la’akari da yadda ba sa ga-maciji da juna.

Sai dai Shehin malamin ya ce ziyarar na cike da tarihi kuma za ta bunkasa fahimtar juna, ’yan uwantaka da zaman lafiya tsakanin mabiya bangarorin biyu.

Sheikh Abdullahi, bayan jinjina ga tsarin koyarwar makarantar, inda ko a kwanakin baya aka samu wata daliba ’yar asalin kasar Faransa ta haddace Alkur’ani a cikinta, ya ce babban burinsa shi ne yada ilimin Alkur’anin, ko da kuwa da wacce kungiya ko darika ce.

Malamin, wanda kuma shi ne Daraktan makarantar Almuyassar Litahfizil Qur’an da ke birnin Dakar a kasar Senegal, ya ce a shirye suke tsaf su fara shirin musayar dalibai da makarantar ta Nurul Tilawa don bunkasa fahimtar juna tsakanin Musulmai.

“Na jima ina bibiyar harkokin wannan makarantar a shafukanta na sada zumunta, sai na lazimta wa kaina cewa zan zo kafa da kafa. Na yi amanna ta hanyar musayar daliban da sauran makamantan shirye-shirye, za mu kara hadin kai tsakanin Musulmai sannan mu rage gaba ta ba gaira ba dalili a tsakanin yara da matasa,” inji shi.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban makarantar ta Nurul Tilawa, Sheikh Nura Umar Tahir, ya ce babu makawa shirin zai taimaka wajen hada kan Musulmai.

Ya yi alkawarin hada kai da malamin wajen shirye-shirye da dama, ciki har da shirya tarukan kara wa juna sani da bitoci da kuma makaloli don kawar da gaba tsakanin Musulmai.