✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara makala wa jami’an tsaro kyamara a jikinsu

Za a makala kyamarori a jikin jami’an tsaro domin nadar duk wani motsinsu a yayin da suke aiki

Majalisar Wakilai ta bukaci a rika sanya wa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro kyamarori a jikinsu domin nadar duk wani motsinsu a yayin da suke gudanar da ayyukansu domin hana su wuce gona da iri.

Dokar da Majalisar ke kawowa ta kuma bukaci a kafa cibiyoyin sanya ido a kan ayyukan jami’an tsaron domin sanin halin da suke ciki a ko’ina, saboda yadda ake wayan zargin su da cin zali da kuma wuce gona da iri da sunan duganar da aikinsu.

Da yake karin haske kan sabuwar dokar, dan Majalisar Wakilai, Honorabul Abubakar Yunsu, ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa makasudin dokar shi ne, “Tabbatar da aiki ingantacce, bisa tsari ba tare da wata kumbiya-kumbiya da cuku-cuku irin na jami’an tsaro ba.”

Ya ce yin hakan ya zama dole, idan aka yi la’akari da yawan koken da ’yan Najeriya ke yi na zargin ’yan sanda da amfani da karfi fiye da kima a kansu.

Bugu da kari, ana yawan zargin ’yan sanda da aikata kisa babu gaira, babu dalili, “Kuma yawanci idan hakan ta faru sai ka ji sun ce wai an yi ne domin tsare kansu,” inji Honorabul Abubakar.

Wuce gona da iri

Dan majlisar ya ce baya ga ’yan sanda akwai lokutan da ake samu jami’an kwastamsun harbe mutum har lahira a shingen binciken ababen hawa.

Ana dai yawan zargin jami’an tsaro a Najeriya da amfani da karfi fiye da kima a kan fararen hula, ko ma yin kisa gaba-gadi da sunan aiki.

Hakan ne ya kai ga boren EndSARS da ’yan Najeriya suka yi a 2020 na neman a soke rundunar ’yan sanda mai yaki da ayyukan fashi  (SARS) wadda jami’anta suka yi kaurin suna a wajen yawancin mutane a matsayin masu kisan gilla da cin zali da suna bincike.

Bugu da kari, ana yawan zargin jami’an tsaro da roko da kuma karbar na goro, hatta a bainar jama’a.
Akwai kuma lokuta da aka zargi wasu da hada baki da masu aikata miyagun laifuka da kuma hada baki da masu aikatawa.

Sai dai kuma hukumomin tsaro sun sha nanata cewa ba za su yi wata-wata ba, wajen hukunta dun wani jami’i da aka samu da duk wani nau’i na saba ka’idar aiki, cin zali, wuce gona da iri da sauranu.

Hasali ma, suna kira ga jama’a da su rika kawo rahoton duk jami’in tsaron da ke aikata irin hakan domin ya fuskanci hukunci, ba sani, ba sabo.