Gamayyar Kungiyoyin Masu Sayar da Amfanin Gona (NECAS), reshen Jihar ta kafa wani kwamiti da ya kunshi jami’an tsaro da zai fara kwato bashin da aka ba manoma a Jihar.
Bayanai sun nuna an ba manoman bashin ne tun a shekarun 2018 da 2019, karkashin shirin CBN-ABP.
- Ambaliya ta lalata gidaje kusan 150 a Jos
- An lakada wa Kwamishina duka a wajen rabon kayan tallafi a Ondo
Shugaban kungiyar ta NECAS reshen jihar Yobe, Hon Nuhu Baba Hassan ya ce kwamitin ya kunshi jami’an tsaron farin kaya na DSS, ’yan sanda da Jami’an Sabil Difens da sarakunan gargajiya.
A cewar Shugaban, ya kamata a biya kudin da tsabar kudi ko da kayayyaki kamar yadda aka amince tun farko a cikin yarjejeniyar lamuni da aka yi tsakanin kungiyar da wasu manoman Jihar.
Don haka ana sanar da manoman da suka ci gajiyar shirin don biyan bukatun kansu da su gaggauta biyan bashin da ake bin su gaba daya, don gujewa fuskantar fushin hukuma.
A cewar shi, “Matukar wanda ya karbi wannan rance ya gaza zuwa don biya to kuwa babu makawa ya za a tuntubi mutumin da ya tsaya masa, don dawo da duk wasu kudade da kayayyakin da aka ba shi, kamar yadda aka amince da su a cikin fom ɗin da aka cike mai dauke da sharudda kafin bada rance.”
“Wannan matakin ya zo ne sakamakon umarnin da mai girma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da cewa dole ne ku dawo da bashin duka, ba wani bangare na shi ba.”