Hukumar karbar Korafi da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano ta fara shirye-shiryen kayyade farashin kayan masarufi a Jihar.
Hukumar ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwa marasa kishi ke tayar da farashin kaya babu gaira, babu dalili, kuma ta ce za ta sa kafara wando guda da miyagun ’yan kasuwar.
- Fulani sun fi kowa shan wahalar masu garkuwa da mutane — Bagudu
- ASUU ta yi barazanar maka DSS a gaban kotu
“Halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu ne ya sa muka ga dacewar mu shigo mu saita wa ’yan kasuwa farashin kayan masarufi, musamman kayan abinci,” inji Shugaban Hukumar, Mahmoud Balarabe.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa hakan ya zama dole ne ganin yadda wasu tsirarun ’yan kasuwa ke tayar da farashin kayan masarufi, wanda ke ta jefa rayuwar mutanen Jihar Kano cikin kunci.
A don haka hukumar ba za ta kyale miyagun ’yan kasuwar su ci gaba da kuntata wa rayuwar mutanen Kano ba, baya ga kuncin rayuwar da ake fama da ita a Najeriya.
“Hukumarmu na aiki tare da Majalisar Dokokin Jihar Kano domin yin gyaran fuska da nufin kara wa hukumar tamu karfi.
“Daga cikin dokokin har da dokar da za ta taka burki ga yadda wasu ’yan kasauwa suke tayar da farashin kayan masarufi haka kawai,” inji shi.
Ya ba da tabbacin cewa hukumar za ta kiyaye doka wajen aiwatar da aikin kayyade farashin kayayyakin.