Nan ba da jimawa ba za a fara aikin hako ma’adinin ‘Uranium’ wanda ake iya amfani da shi wajen hada makamin Nukiliya a karon farko a Najeriya.
Za a fara aikin hakan ne a yankin Mika da ke Karamar Hukumar Yorro ta Jihar Taraba.
- Fasto ya kwace mata da ’ya’yan abokinsa ya damfare shi N105m
- Amurka ta gana da sojojin da suka yi wa Bazoum juyin mulki a Nijar
Wani kamfani mai suna Clarisver Solution, ne ya samu lasisi daga Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya don hako ma’adinin.
Leonard Kemalolam, mai ba da shawara kan Muhalli ga kamfanin na Clarisver, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta shirya.
A yayin taron da aka gudanar a Jalingo a ranar Talata, ya ce wannan wani bangare ne na aikin Hukumar Kula da Nukiliya ta Najeriya.
Kemalolam, ya sanar da cewar taron ya samu halartar jami’an ma’aikatar muhalli ta jihar Taraba, da hukumar kula da makamashin nukiliya ta Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki da suka karbi bakuncin taron.
“Lasisi kan hakar Uranium na kan ka’ida daga Hukumar Kula da Nukiliya ta Najeriya karkashin Dokar Kare Nukiliya mai lamba 9 ta 1995.
“Sauran manufofin su ne tantance tasirin muhalli na shirin aikin hakar Uranium da ake shirin yi a jihar Taraba, da hada kan al’umma da masu ruwa da tsaki wadanda aikin zai shafa,” in ji shi.
Da yake tsokaci game da aikin, wakilin Sarkin Kwaji, yankin da ma’adinin yake, Alhaji Gabdo ya ce kafin kamfanin ya fara aikinsa dole ne ya tabbatar da tsaron daukacin al’ummar yankin tare da biyan su diyya.
Ya ce dole ne kamfanin ya cika alkawarin da ya yi wanda ya hada da daukar kaso 60 cikin 100 na ma’aikatansa da kuma samar da ababen more rayuwa da suka hada da ruwa, hanyoyi, makarantu da wuraren kiwon lafiya.
Shi ma da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin nazari kan EIA, Alhaji Kasimu Bayero, ya ce aikin yana da fa’ida ga tattalin arziki ga jihar Taraba da Najeriya domin zai samar da karin hanyoyin samun kudin shiga na kasashen waje.