kungiyar da ke shirya harkar kwallon tennis da aka fi sani da Dala Hard Court Championship ta bayyana cewa ta gama shirinta tsaf don tunkarar gasar wasan kwallon tennis na bana wanda shi ne karo na 28. A cikin takardar da ta raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren shirye-shiryen gasar Yusuf Datti, kungiyar ta bayyana cewa za ta fara gudanar da gasar gwaje ce watau (Preliminaries) a ranar 5 zuwa 7 ga watan Disamba, kafin daga bisani a cigaba da gudanar da babbar gasar a ranar 8 ga watan Disamba.
kungiyar ta shawarci Hukumar wasan kwallon Tennis ta kasa (NTF) da ta gayyato maza 20 da mata 10 da suka fara yin wasan don halartar babbar gasar. Har ila yau kungiyar ta bayayna cewa Bankin First bank da Bankin Fedility da kuma jihohin Kano da Jigawa su ne jiga-jigan da za su dauki nauyin gasar sai kuma wasu kamfanoni da daidaikun mutane da suka hada da Alhaji Isyaku Umar Tofa (dan Adalan Kano).
kungiyar ta bayyana cewa tana alfahari da kasancewarta kungiya daya tilo a duk fadin jihohin Arewa da take ci gaba da gudanar da harkokinta tsawon shekaru 28. Kamar yadda aka saba, kungiyar ce za ta dauki nauyin abinci da na masaukin shugabannin da ake sa ran za su halarci gasar da kuma na ‘yan wasa.
Haka kuma a cewar kungiyar Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso shi ne zai zama bako na musamman a wajen bikin rufe gasa.
Za a fara gasar kwallon tennis na Dala ta bana a Kano
kungiyar da ke shirya harkar kwallon tennis da aka fi sani da Dala Hard Court Championship ta bayyana cewa ta gama shirinta tsaf don tunkarar…