Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta ce daga yanzu zata fara cin tarar masu sare bishiyoyi ba tare da izini ba, ko dai a gidajensu ko kuma a muhimman wuraren taruwar jama’a tarar N100,000.
Darakta a Sashen Kula da Wuraren Shakatawa ta hukumar, Misis Riskatu Abdulaziz ce ta sanar da hakan lokacin da take rangadin duba manyan bishiyoyin da aka dasa a tsakiyar birnin ranar Lahadi.
- Asibitin Aminu Kano ya gudanar da dashen dodon kunne na farko
- An mayar da ’yan Arewa 42 gida daga Ondo
A cewarta, duk bishiyar da aka shuka a gida, daga lokacin da ta girma ta zama mallakin al’umma, hakan ya sa dole ana bukatar izinin hukuma kafin a sareta.
Misis Riskatu ta ce gwamnati na yunkurin dakile illolin sauyin yanayi a birnin, inda ta ce ba za su zura ido su bari mutane su ci gaba da jefa rayuwar al’umma cikin hatsari ba.
Ta kara da cewa ko da an sare bishiyar da izinin hukumar, dole a sake dasa wata domin maye gurbinta, tana mai cewa ba ana dasa bishiya domin kare muhalli kawai ba ne, har ma da kawata muhallin.
Ta ce, “Duk wanda ya sare bishiya ba bisa ka’ida ba, ya danganta da girma da kuma shekarun bishiyar, zai biya tarar N100,000, sannan a tilasta masa shuka wasu guda biyu a madadinta.
“Bishiya na da matukar muhimmanci ga dan Adam, saboda ita ce take samar da iskar da muke shaka sannan ta yi amfani da wacce muke fitarwa,” inji ta.
Bugu da kari, ta ce bishiya na kuma rage hayaniya a muhalli sannan tana taka muhimmiyar rawa wajen kare illolin dumamar yanayi.