Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya amince a fara biyan ’yan fansho mafi karancin albashin N12,000 duk wata.
Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Hussain Ali Kila, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis.
- Muna da gibin likitoci 3,000 –Gwamnatin Neja
- Hare-haren ’Yan Bindiga: A Tallafa Mana Da Muhalli —Katsinawa
Ya ce gwamnatin za ta rarraba wa masu ruwa da tsaki sanarwar amfani sabuwar dokar, domin fara aiwatarwa daga watan Janairun 2023.
Kafin wannan sabon tsarin dai, ana biyan ’yan fanshon N5,000 ne a matsayin mafi karancin albashi.