✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara biyan matasa marasa aikin yi har sai sun samu a Algeria

Akwai marasa aikin yi 600,000 a kasar.

Shugaban Algeria ya ce zai bullo da tsarin biyan matasan da ba su da aikin yi a kasar yayin da take fama da adadin marasa aikin.

BBC ya ruwaito Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya fada wa ’yan jarida cewa za a fara biyan matasan ’yan shekara 19 zuwa 40 daga watan Maris.

Wadanda suka cancanci shiga tsarin za su karbi kudin da ya kai kusan dala 100 duk wata, da kuma wasu tallafi na lafiya, har sai sun samu aikin yi.

Da yake ba da sanarwar, Mista Tebboune ya ce Algeria ce kasa ta farko da ta fito da irin wannan shiri wadda ba ta Turai ba.

Ya kara da cewa akwai marasa aikin yi 600,000 a kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, alawus din da za a rika biyan matasan zai kai kusan kaso biyu cikin uku na mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata a kasar da ya kai dinari dubu 20.