Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince a biya dalibai ’yan asalin Jihar da ke karatu a makarantun gaba da sakandaren kasar nan kudaden tallafin karo karatu.
Kimanin dalibai 38,183 ne ake sa ran za su ci gajiyar tallafin.
- Yadda duba wayar miji miji ba izini ya jawo wa mata dauri a kurkuku
- Najeria A Yau: Rikicin Majalisar Malaman Kano ya bar baya da kura
Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar ba da tallafin karo karatun dake Damaturu, Tijjani Ciroma da ya aikewa manema labarai ranar Litinin.
A cewarsa, hukumar ta sanar da dukkan daliban dake karatu a jami’o’i da kwalejojin ilimi cewa gwamna Buni ya amince a biya su kudin tun a ranar takwas ga watan Oktoban 2021.
“Hukumar za ta yi zama da shugabannin daliban a mako mai zuwa don zayyana hanyoyin da za a bi wajen tantance daliban, sannan a tsara yadda za a fara biyansu kudaden,” inji sanarwar.
Daga nan hukumar ta ce za ta sanar da dukkan bangarorin dalibai da duk bayanan da suka dace kan tsare-tsaren nasu nan ba da jimawa ba.