Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya sanar cewa muddin aka kashe takwaransa na Jihar Binuwe, Samuel Ortom, to kuwa alhakin jininsa zai rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya.
A ranar Asabar da ta gabata ce aka kai wa gwamnan na Benuwe hari, inda wasu ’yan bindiga suka bude wa ayarin motocinsa hari a kan hanyar Makurdi zuwa Gboko da ke Karamar Hukumar Makurdi ta jihar.
- Babu hannun Fulani a harin da aka kai wa Gwamnan Binuwai – Miyetti-Allah
- Na yi nadamar goyon bayan Buhari a 2015 – Dino Melaye
A yayin da yake martani dangane da lamarin a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, Wike ya ce idan har aka kashe gwamnan Benuwe, to akwai yiwuwar a sake fafata wani yakin basasa a kasar nan.
A cewarsa, “Idan kun kashe Ortom, to ku shirya yi wa Najeriya jana’iza. Don muddin wani abu ya sami Gwamna Ortom, alhakinsa zai rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya ne kuma ta tabbata ta zauna cikin shiri don Najeriya za ta gushe daga kasancewa.”
Wike ya kuma yi zargin cewa a lokacin babban zaben kasa na 2019, tsohon Kwamandan rundunar sojin kasa a shiyar Fatakwal, Manjo Janar Jamil Sarham da kuma wasu kusoshin jam’iyyar APC sun kammala shirin kawar da shi daga doron kasa.
Ya bayyana damuwa a kan lamarin yadda rayuwar gwamnoni ke ci gaba da fuskantar barazana ya zama ruwan dare a kasar nan.