Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya amince gwamnatin jihar Zamfara ta debi matasa 7,500 a masatyin kuratan ‘yan sandan domin aikin samar da tsaro a yankunansu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Alhaji Usman Nagoggo shine ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga rukunin farko na matasan a Gusau ranar Alhamis.
- ‘Yan sanda sun cafke mata da miji da kan mutum a Ogun
- Samar da tsaro: Zamfarawa 3,850 sun fara samun horo
Ya ce daga cikin adadin, tuni ‘yan sanda suka tantance mutum 3,850 a matsayin rukuni na farko.
Kwamishinan ya ce, “Za mu kaisu zuwa makarantun horar da jami’anmu na jihohin Sakkwato da Kaduna domin samun horo na tsawon watanni biyu, inda daga nan ne za su dawo jihar a watan Disamba, sannan mu sake tura wani rukunin.
“Dukkan wadanda suka sami nasarar shiga aikin wasu muhimman mutane ne daga yankunansu suka zabo su saboda cancantarsu.
“Idan mun tuna a bara, babban Sufeton ‘Yan Sanda ya kaddamar da shirin shigar da sauran al’umma cikin samar da tsaro a yankunansu,” inji Nagoggo.
Ya kuma ce Zamfara ce jiha ta farko a fadin Najeriya da ta fara kaddamar da shirin da mutane masu yawa, inda ya ce suna sa ran ganin sauyi cikin harkokin tsaron jihar da zarar matasan sun kammala samun horon.
Daga nan sai ya yi kira ga sabbin ‘yan sandan da su kasance jakadun jihar da ma na kasar nagari, yana mai cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashawa ko alaka da ‘yan bindiga ba.
Shi kuwa da yake jawabi a madadin gwamnatin jihar, kwamishinan watsa labarai na jihar, Alhaji Sulaiman Tunau ya ce shirin na daya daga cikin kudirorin gwamna Bello Matawalle na magance matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Ya ce matasan, wadanda gwamantin jihar ce za ta rika biyansu albashi a kowanne wata za su fito ne daga dukkan kananan hukumomin jihar guda 14.
Alhaji Sulaiman ya kuma ce baya ga magance kalubalen tsaro, shirin zai kuma samar da ayyukan yi ga matasa.