Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta tura matasa ’yan asalin Jihar, akalla mtuum 4,000 domin samun horon aikin dan sanda a cikin al’umma.
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne a yayin karbar bakuncin Shugaban Kwalejin Kananan Hafsoshin Dan Sanda da ke Wudil a Jihar, Lawal Tanko-Jimeta a ranar Alhamis.
- Sabuwar Dokar Tsarin Neman Aure a Kano
- An gano bom a makarantar firamare a Najeriya
- Dalibi ya yi doguwar suma bayan yi masa bulala 6,000
- Damfarar N450m: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi —Ummi Zee-zee
“Duk lokacin da wata hukumar tsaro za ta dauki aiki, to Jihar Kano ta riga ta tanadi wadanda za ta iya dauka a kasa,” inji Gwamnan.
Ya ce a baya-bayan nan, Gwamnatin ta tura wasu matasan Jihar domin ba su horon aikin dan sanda a yunkurin jihar na shirya su domin aikin samar da tsaro a cikin al’umma.
A cewarsa, Gwamnatin ta samar da cibiyar kula da bayanai a Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar inda ta samar da kyamarorin kan hanya domin lura da abubuwan da ke faruwa a cikin gari.
Ya ce baya ga haka, gwamantin ta samar da wasu cibiyoyin tsaro a kan manyan hanyoyin da suka sada jihar da wasu jihohin
“Da haka za mu iya lura da abubuwan da ake shigo da su ko ake fita da su daga garin Kano.
“A Dajin Dansoshiya da ke makwabtaka da Jihar Katsina kuma, mun kafa wa makiyaya rufage na zamani masu dauke da abubun da ake bukata da kayan tabbatar da samar da ilimi ga ’ya’yansu.
“Ta wadannan hanyoyin za mu iya rage matsalolin tsaro a Jihar Kano,” inji gwamnan.
Tun da farko, sai da Shugaban Kwalejin ’Yan Sandan ya yaba da irin hadin kan da kwalejin take samu daga Gwamnatin Kano da al’ummar da ke makwabtaka da ita.
Ya kuma bukaci gwamnan da ya taimaka wajen ginawa da kuma yin kwaskwarima ga dakunan kwanan daliban Kwalejin.
“Wasu dakunan kwanan sun tsufa sun lalace, muna aiki da masu ruwa da tsaki a Gidauniyar Tallafa wa Ilimi Mai Zurfi (TETFUN) domin ganin an inganta kayan aiki a Kwalejin,” inji shi.