✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a dauke wuta tsawon awa 8 a Kano, Katsina da Jigawa —KEDCO

Za a dauke wutar ce daga karfe 10 na safe zuwa 6:30 na yamma ranar Asabar

wwwwKamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya ce zai dauke wuta na tsawon sa’a takwas a jihohin Kano da Katsina da Jigawa ranar Asabar.

Mai magana da yawun KEDCO, Ibrahim Sani Shawai, ya ce za a dauke wutar ce daga misalin karfe 10 na safe zuwa 6:30 na yamma domin gudanar da gyara a tashar lantarki da ke Kumbotso.

KEDCO, wanda ke samar da wutar lantarki a jihohin Kano, Katsina da Jigawa, ya c,e “Hakan zai bayar da damar gudanar da gyara a tashar lantarki da ke Kumbotso, wadda ke ba wa Kano wutar.

“Gyaran da za a yi zai inganta samuwar wutar lantarki ga abokan huldarmu,” in ji sanarwar da kamfanin ya fitar.

Kamfanin ya ba wa jama’a hakuri da kuma tabbacin cewa da zarar an kammala gyaran za a dawo da wutar.