Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA za ta binciki tsohon dan wasan kasar Sweden, Zlatan Ibrahimovic kan zargin hada hannu wajen mallakar wani kamfanin caca.
Wasu rahotanni daga Sweden na cewar dan kwallon na kungiyar AC Milan, mai shekara 40 ya karya ka’idar hukumar, bayan da ya yi hadakar hannun jari mallakar kamfanin caca.
- Matasa sun kashe ’yan bindiga a Sakkwato
- Rashin tsaro: Addu’o’in da za a yi a Ramadan —Sarkin Musulmi
Jaridar Aftonbladet ta ruwaito cewa, a halin yanzu dan wasan yana cikin tsaka mai wuya yayin da ake zarginsa kan sanya hannu jarin a wani kamfanin caca.
Zlatan ya mallaki kashi 10 cikin 100 na Bethard, wani kamfanin caca mai tarin ofisoshi a kasar Malta.
A dokar Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ba a amince wani dan wasa ya zuba jari ko hannu a kamfanin caca ba.
Jaridar Sun ta yi ikirarin cewa, dokoki da’a da FIFA ta gidanya sun nuna cewa, duk wanda ya karya ka’idodin zai fuskanci hukuncin tara da kuma dakatar da shi daga duk wasu harkokin da suka danganci kwallon kafa na tsawon shekara uku.
A makon shekaran jiya ne Ibrahimovic ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a AC Milan, bayan da ya cika shekara 40 da haihuwa.
Tsohon dan wasan, wanda ya buga wa kungiyoyin Manchester United da Barcelona, da Inter Milan da PSG, ya ci kwallo 17 a wasa 25 a dukkan fafatawar da ya yi a kakar bana.
Yana cikin ’yan wasan da suka buga kungiyoyin kwallon kafa a duniya, inda ya zagaye kasashe da dama.
Makonni biyu da suka gabata ne kuma aka samu rahoton cewa Ibrahimovic ya amince ya koma buga wa kasarsa ta Sweden bayan shekara biyar da yin ritaya.