’Yan sanda a Ingila suna tuhumar dan kwallon kulob din Chelsea Danny Drinkwater bayan an same shi da laifin yin tuki bayan ya yi tatil da giya inda ya haddasa hadari a tsakaninsa da wata mota.
Al’amarin ya faru ne a wayewayar garin ranar Litinin da ta gabata, bayan dan kwallon ya halarci wani biki da aka kwana ana cashewa a wani otel da ke Landan.
A yayin bikin ne dan kwallon ya yi tatil da giya sannan ya tuka mota zuwa gida, kuma a kan hanyarsa ce ya yi taho-mu-gama da wata mota wanda hakan ya janyo aka samu raunuka ciki har da dan kwallon.
Jami’an tsaro sun ce tuni suka kama dan kwallon kuma da zarar sun gama bincike za su kai shi kotu don a yanke masa hukunci.
Laifi ne babba mutum ya sha giya sannan ya tuka mota a Ingila. Hakan zai iya sa a ci tararsa makudan kudi idan kotu ta tabbatar da laifin.
Drinkwater dai yana daga cikin ’yan kwallon Chelsea da ke buga wasa a tsakiyar fili.