Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) reshen Jihar Kano, ta ba da tabbacin samar da isasasshen mai a jihar, duk da matsalar safara da aka samu sakamakon zanga-zangar #EndSARS a Najeriya.
Shugaban reshen, Alhaji Bashir Danmalam ne ya bayyana wa manema labarai hakan, duba da matsalar karancin man fetur da wasu jihohi ke fuskanta, ciki har da Birnin Tarayya Abuja, inda matsalar ta fi kamari.
- Yadda ake fargabar karancin man fetur a Abuja
- Sanatoci sun yi kira ga gwamnati akan karancin man fetur
- Jawabin Buhari kan farashin man fetur ya janyo cece-kuce
Ya ce babu bukatar mutane su damu domin kungiyar ta yi tsare-tsaren samar da wadataccen man fetur ga jihohin da ke shiyyar da suka hada da Kano, Katsina, Bauchi, Yobe da Jigawa.
Alhaji Bashir Danmalam ya yaba wa Daraktan Gudanarwar Man Fetur na Kasa, Lawal Musa da ya ba da damar ci gaba da rarraba man fetur a fadin Najeriya bayan cikas da zanga-zangar #EndSARS ta haifar.