✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gombe: Za a bude masallatai da majami’u daga ranar Juma’a

Gwamantin Gombe ta dage dokar da ta sa ta kulle masallatai da majami’u a jihar dan hana yaduwar cutar Coronavirus a jihar. Gwamnan jihar Inuwa…

Gwamantin Gombe ta dage dokar da ta sa ta kulle masallatai da majami’u a jihar dan hana yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

Gwamnan jihar Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da shugabanin addini a kan janye dokar, inda ya ce ranar Juma’a za a  bude wuraren ibadun da aka kulle.

Ya ce jama’a sun matsa sai an bude wuraren ibada don haka za a bude amma da sharadin kiyaye wanke hannu da sanya takunkumin fuska.

Inuwa Yahaya ya kuma ce saboda kare lafiyar al’ummar ya sanya wannan dokar ba don son ransa ba.

“Zan iya sauka a kujerar gwamna don jama’a ta su samu lafiya”, in ji shi.

Tuni dai jami’an tsaro suka fara bai wa ‘yan agaji da ‘yan Boys Brigade horo a kan yadda za su tabbatar da ba da tazara a masallatai da majami’u.