Gwamantin Gombe ta dage dokar da ta sa ta kulle masallatai da majami’u a jihar dan hana yaduwar cutar Coronavirus a jihar.
Gwamnan jihar Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da shugabanin addini a kan janye dokar, inda ya ce ranar Juma’a za a bude wuraren ibadun da aka kulle.
Ya ce jama’a sun matsa sai an bude wuraren ibada don haka za a bude amma da sharadin kiyaye wanke hannu da sanya takunkumin fuska.
- Coronavirus: Majinyata sun yi zanga-zanga a Gombe
- COVID-19: Gwamnatin Gombe ta dakatar da sallar jam’i
Inuwa Yahaya ya kuma ce saboda kare lafiyar al’ummar ya sanya wannan dokar ba don son ransa ba.
“Zan iya sauka a kujerar gwamna don jama’a ta su samu lafiya”, in ji shi.
Tuni dai jami’an tsaro suka fara bai wa ‘yan agaji da ‘yan Boys Brigade horo a kan yadda za su tabbatar da ba da tazara a masallatai da majami’u.