✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a bude filayen jiragen sama biyar

Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin bude filayen jiragen sama guda biyar a fadin Najeriya daga ranar 21 ga watan Yunin da muke ciki. Darekta…

Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin bude filayen jiragen sama guda biyar a fadin Najeriya daga ranar 21 ga watan Yunin da muke ciki.

Darekta Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) Kyaftin Musa Nuhu ya bayyana  cewa tashsoshin jiragen da za a bude sun hada da:

  • Baban Filin Jirgi na Murtala Mohammed International (MMIA), Legas;
  • Babban Filin Jirgi na Nnamdi Azikiwe International, Abuja;
  • Babban Filin Jirgi na Mallam Aminu Kano; sai kuma
  • Babban Filin Jirgi Fatakwar, Omagwa Jihar Ribas;
  • Filin Jirgi na Sam Mbakwe, Owerri.

Sanarwar da NCAA ta aike wa kamfanonin jiragen sama masu aiki a Najeriya ta wajabta cika ka’idojin kare yaduwar cutar coronavirus a kan dukkan jiragen masu sauka da tashi a filayen biyar.

Kyaftin Musa Nuhu ya ce daga baya za abude karin filayen jiragen sama bayan an tabbatar da matakan kariyar cutar a filayen.

Sai dai ya kara da cewa filayen da za a bude za su ci gaba da zama a rufe har zuwa ranar 21 ga watan Yunin da za a sake bude su.

A ranar 27 ga watan Maris ne Gwamnatin Tarayya ta rufe filayen jiragen sama a wani mataki na dakile yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya.