Shugaba Buhari ya ba da umarnin biyan ’yan fanshon Gwamnatin Tarayya karin kudadensu tun daga shekarar 2019.
Hukumar Kula da Fansho ta Kasa (PTAD), ta ce za a biya ’yan fanso bashin karin da aka yi musu ne tun daga watan Afrilun 2019.
- Hattara dai mata: Mu yi wa kanmu fada kafin ranar da-na-sani
- Batanci ga Sahabbai: An dakatar da malami daga yin wa’azi a Bauchi
- ’Da kyar muke samun abinci a azumin bana’
“Da wannan izinin, PTAD ta samu karfin yin kari ga dukkannin hakkokin ’yan fansho,” inji Shugabar Hukumar, Chioma Ejikeme.
Ta ce daga watan Mayun 2021 za a fara biyan su bashin kudaden, a kuma ci gaba da biyan hakkokin ’yan fanshon bisa sabon tsarin albashin ma’aikata na shekarar 2019.
Shugabar ta jaddada cewa PTAD ba za ta bukaci ko sisi daga hannun ’yan fansho a matsayin na goro ba, kafin a biya su hakkokinsu.
Don haka ta shawarce su da su yi hattara kar su fada hannun ’yan damfara da masu ci da gumin wasu.