Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da biyan Naira biliyan 13.3 a matsayin inshora ga ’Yan Sandan Najeriya da suka mutu.
Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi, ya ce jami’ai 318,319 ne za su ci gajiyar shirin tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023.
- Ni zan jagoranci yi wa Tinubu kamfe a sabuwar shekara —Buhari
- Mataimakiyar Gwamnan CBN ta bayyana a gaban Majalisa
A cewarsa, an samar da shirin inshorar ne don karfafa wa ’yan sanda gwiwa a aikin da suke yi babu dare, babu rana don kare rayuka da dukiyar ’yan kasa.
Ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan kammala taron Majalisar a Fadar Shugaban Kasa ranar Laraba.
Taron Majlisar ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.