Hukumar ’Yan Sandan Najeriya PSC ta sanar da yi wa wasu manyan jami’anta karin girma ciki har da tsohon mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ibrahim Magu.
A ranar Litinin ce mai magana da yawun Hukumar ta PSC, Ikechukwu Ani ya sanar da karin girman da aka yi wa Magu wanda aka daga likafarsa zuwa mukamin Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan sanda (AIG).
- ‘Yan bindiga sun kashe Sojoji biyu, sun kone Kotu a Anambra
- Yadda dubun wasu masu garkuwa da mutane ta cika a Kaduna
Ya ce an yi wa Magu karin girman ne tare da wasu manyan jami’ai yayin taron da Hukumar ’Yan Sandan ta gudanar karo na 15 a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce an tabbatar da DIG John Ogbonnaya Amadi a matsayin Babban Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (DIG) wanda kafin yanzu yake zaman mukaddashi.
Haka kuma shi ma Zama Bala Senchi an daga likafarsa a matsayin Babban Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (DIG).
Hukumar ’Yan Sandan ta kuma amince a daga likafar Manyan Mataimakan Kwamishonin ’Yan Sanda 23 zuwa mukamin Kwamishinan ’Yan Sanda; Mataimakan Kwamishonin ’Yan Sanda 31 zuwa Manyan Mataimakan Kwamishonin ’Yan Sanda; da kuma Manyan Sufurtandan ’Yan Sanda 63 zuwa mukamin Mataimakan Kwamishonin ’Yan Sanda.
Sauran Kwamishonin ’Yan Sandan da Hukumar PSC ta amince a yi wa karin girman tare Magu zuwa mukamin Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da suka hada da Abraham Egong Ayim da Okunlola Kola Kamaldeen da Andrew Amieengheme da Akeera Mohammed Younous da Celestine Amechi Elumelu da Ngozi Vivian Onadeko da kuma Danladi Bitrus Lalas
An dai shafe tsawon lokaci ana jeka-ka-dawo kan batun daga likafar Ibrahim Magu, wanda aka dakatar kan zargin almundahanar kudade.
A watan Yulin 2020 ne Fadar Shugaban Kasa ta dakatar da Magu tare da bayar da umarnin tsare shi gami da gurfanar da shi gaban wani Kwamitin Bincike da ta kafa bisa jagorancin Mai Shari’a Ayo Salami, inda aka ci gaba da laluben gaskiyar lamari kan tuhume-tuhumen saba ka’idojin aiki, da karkatar da kudaden gwamnati.